1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron sulhu tsakanin gwamnatin Uganda da ´yan tawaye

July 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuqZ
An bude taron samar da zaman lafiya da nufin kawo karshen yakin basasa tsakanin sojojin gwamnatin Uganda da na ´yan tawayen kungiyar Lord´s Resistance Army LRA a garin Juba na kasar Sudan. Dukkan wakilan gwamnati da na ´yan tawaye sun zauna kan teburi guda da Sudan mai shiga tsakanin don yin sulhu. An fara tattaunawar ne bayan an fuskanci kwan gaba kwan baya a babban birnin na yankin kudancin Sudan mai ´yancin cin gashin kai. Shugaban yankin Salva Kiir ya yi kira ga sassan biyu da su yi amfani da wannan dama ta tarihi don kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru 19 ana yi a arewacin Uganda. Ministan cikin gidan Uganda Ruhakana Rugunda ke jagorantar tawagar gwamnati, to amma shugabanin ´yan tawaye sun ki halartar taron na Juba saboda gudun kada kotun kasa da kasa ta birnin The Hague ta sa a kama su. Alkalumma sun nunar da cewa kimanin mutane dubu 100 aka kashe sannan aka tilastwa wasu milyian biyu tserewa daga yankin sakamakon wannan rikici.