1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaben ´yan majalisar dokoki a Timor Ta Gabas

June 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuHc

An bude tashoshin zabe a fadin kasar Timor Ta Gabas inda ake gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki karo na biyu tun bayan samun ´yancin kasar a shekara ta 2002. Jam´iyun da zasu kai labari a zaben sun hada da jam´iyar Fretilin dake jan ragamar mulki da kuma abokiyar adawarta wato jam´iyar sake gina kasar Timor Ta Gabas wadda tsohon shugaban Xanana Gusmao ya kafa. To sai dai babu daya daga cikin jam´iyun biyu da ak yi hasashen zata samu gagarumin rinjayen kujeru 65 na majalisar dokokin da ake bukata don yin mulki ita kadai. Wato kenan bisa ga dukkan alamu sai an yi hadin guiwa da wasu daga cikin jam´iyu 12 da ke takara a zaben na yau.