1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zaman makokin Rasuwar Shugaban Poland a wani hatsarin Jirgin Sama

April 10, 2010

Shugabanni da sauran al'umar ƙasar Poland naci gaba da nuna juyayin su game da rasuwar Shugaban ƙasar ta Poland Lech Kaczynski tare da matar sa Maria

https://p.dw.com/p/MspS
Shugaban Ƙasar Poland Lech KaczynskiHoto: AP

Shugabanni da sauran al'umar ƙasar Poland na ci gaba da nuna juyayin su game da rasuwar Shugaban ƙasar ta Poland Lech Kaczynski tare da matar sa da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar a wani hatsarin jirgin sama a wani gari dake yankin ƙasar Rasha. Marigayi shugaban na Poland tare da tawagar sa suna kan hanyar su ta zuwa bikin cika shekaru 70 da kisan ƙare dangi da sojojin Rasha suka yiwa wasu manyan jami'an sojin Poland, a lokacin yaƙin duniya na biyu. Dukkan fasinjoji 96 da kuma masu hidima na jirgin ne, suka halaka a lokacin da jirgin ya faɗo yana gaf da sauka da sanyin safiyar yau a wani gari dake cikin ƙasar Rasha. A martanin farko bayan hatsarin Firaministan Poland Donald Tusk ya bayyana hatsarin a matsayin wani bala'i da ya aukawa ƙasar tun bayan yaƙin Duniya na biyu. A saƙon ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ministan harkokin waje Guido Westerwelle sun bayyana mutuwar shugaba Kaczynski da cewar, wani rashi ne ga al'umar Poland da Turai da ma duniya baki ɗaya. Shi ma Shugaban Geogia Mikhaila Saakashvilli ya bayyana marigayin da cewar- mutum ne dake son samarwa al'umma 'yanci, mutum ne mai hangen nesa. Yana matuƙar ƙaunar Poland, ɗan Siyasa ne mai ƙaunar jama'a da kuma ƙasar sa, kuma jarumi ne- Firaministan Rasha Vlademir Putin ya bada umarnin gano musabbabin hatsarin Jirgin cikin gaggawabayan yakai ziyara inda hatsarin ya auku. Tuni dai gwamnatin Poland ta ware mako guda domin zaman makokin Rasuwar Shugaban da kuma sauran muƙarraban gwamnatin ƙasar da suka rasu tare da shi.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita:Muhammad Nasiru Awal