1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fitar da sabuwar gwamnati a Birtaniya

Salissou BoukariJuly 14, 2016

Bayan da sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta kaddamar da ita a matsayin sabuwar Firaministan Birtaniya, Theresa May ta sha alwashin shayo kan kalubale a kasar.

https://p.dw.com/p/1JOcu
Großbritannien Theresa May in der Downing Street 10
Theresa May sabuwar Firaministan BirtaniyaHoto: Reuters/S. Rousseau

Tsohon Firaministan David Camaron ya bata shararwarin cewa duk abun da za ta yi, ta kasance mai mafi kusanci da Tarayyar Turai. Tuni dai aka nada Philip Hammond a matsayin Ministan kudin kasar ta Birtaniya wanda kuma ke da matsayin mai mukami na biyu a cikin sabuwar gwamnatin, yayin da tsohon magajin garin birnin London Boris Johnson, ya samu mukamin ministan harkokin waje, sannan Davi David da ke a matayin tsohon sakataran kula da harkokin Tarayyar Turai, ya samu mukamin ministan kula da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

 

Tuni dai Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, da sabuwar Firaministar da Birtaniya suka sha alwashin tafiyar da kyaukyawar hulda a tsakanin su, Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin shima ya ce da shirye yake da su yi tattaunawa mai mahimmanci tsakaninsa da sabuwar Firaministan ta Birtaniya, yayin da shugaban hukumar zartaswa ta Tarayyar Turai Jean-Claud Juncker, ya yi kira ga sabuwar Firaministan da ta gaggauta soma tattaunawa da Tarayyar Turai.