1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gabatar da bikin baje kolin masana'antu a Hannover

April 19, 2004

Kamfanonin dake halartar bikin baje kolin masana'antu na Hannover, wanda shi ne mafi girma irinsa a duniya, na sa ran samun kyakkyawar bunkasa a wannan shekarar da kuma wasu shekaru masu zuwa

https://p.dw.com/p/BvkX
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a zauren bikin baje kolin masana'antu na Hannover
Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a zauren bikin baje kolin masana'antu na HannoverHoto: AP

A hakika dai kamfanonin da suka saka dogon buri akan sakamakon bikin baje kolin masana’antun na birnin Hannover sune wadanda ke kera injuna da na’urori a nan Jamus. A karo na farko gamayyar masana’antun ta gabatar da alkalumanta da suka shafi dukkan kasashen Turai. Alkaluman sun nuna cewar sama da mutane miliyan 23 ne ke aiki a masana’antu 21000 a sassa dabam-dabam na kasashen Turai, lamarin dake yin nuni da cewar kimanin kashi 40% na ma’aikata a duk fadin nahiyar ke aiki a masana‘antun sarrafa injuna a nan Jamus, sai kuma wasu kashi 19% a kasar italiya. Wani abin da ya taimaka wannan bangaren na tattalin arzikin kasa yake samun bunkasa shi ne fadada laimar kungiyar tarayyar Turai da aka yi domin ta hada da kasashen gabacin nahiyar. Wannan ci gaba ba kawai ya shafi kayayyakin da ake fitarwa ba ne kazalika har da wadanda ake shigowa da su kamar dai wasu bangarori na kayan gini. Shugabar gamayyar masana’antun kera injunan Diether Klingelnberg yayi hasashe yana mai cewar:

Wannan bangaren yana da kyakkyawar makoma dangane da ci gaban al’amuran fasahar sarrafawa. Kazalika sakamakon da aka samu ta fuskar tattali yana ba da kwarin guiwa bisa manufa. A cikin watanni ukun da suka wuce an samu karuwar yawan kwantaragi da misalin kashi 15% fiye da yadda lamarin ya kasance shekarar da ta wuce. A takaice wannan bangare na sa ran samun bunkasar kashi 2% ga ayyukansa.

To sai dai kuma uwar kungiyoyin masana’antun Jamus ba ta zaton cewar kasar zata samu bunkasar kashi 2% ga tattalin arzikinta a wannan shekarar da muke ciki ko da yake zata dan zarce abin da ta samu shekarar da ta wuce, kamar yadda aka ji daga bakin Michael Rogowaski, shugaban gamayyar masana’antun a zauren bikin baje kolin Hannover. Musabbanin haka kuwa shi ne koma bayan da aka samu ga yawan abin da mutane ke kashewa a kasar sakamakon matsalar rashin aikin yi dake addabarta. Wannan matsalar ta ki ci ta ki cinyewa duk kuwa da bunkasar kasuwa da kamfanonin sarrafa injuna ke samu. A yayinda a bangare guda ake neman injiniyoyi ruwa a jallo, amma daya bangaren kananan ma’aikata na ci gaba da asarar guraben ayyukansu. A dai shekarar da ta wuce mutane kimanin dubu 870 suka samu aiki a masana’antun sarrafa injuna a nan kasar ta Jamus. Yawan injinoyoyi da masana fasahar na’ura mai kwakwalwa ta computer da suka samu aiki a wadannan masana’antu ya kai mutum dubu 140 a shekarar ta 2003. Da yawa daga kamfanonin sun hakikance cewar zasu ci gaba da neman karin injiniyoyi daga nan har ya zuwa shekara ta 2009. Wani abin lura kuwa shi ne kasancewar kanana da matsakaitan kamfanoni ne ke sa ran samun bunkasar yawan injiniyoyinsu duk kuwa da cikas da suke fuskanta wajen samun rancen kudaden jari daga bankuna.