1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gabatar da sabon daftarin kuduri don fadada kwamitin sulhu

January 6, 2006
https://p.dw.com/p/BvDc

Kasar Brazil ta ce da ita da kasashen Jamus da Indiya sun gabatar da wani sabon daftarin kuduri don fadada yawan membobin kwamitin sulhu na MDD. Daftarin kudurin yayi kama da wanda kasashen Brazil, Jamus, Indiya da kuma Japan wato ´yan kungiyar G4 suka gabatar a bara, to amma ya gaza samun goyon bayan kashi 2 cikin 3 na wakilan babbar mashawartar MDD. Daftarin ya fuskanci adawa musamman daga Amirka da China, dukkansu membobin dindindin a cikin kwamitin sulhun mai wakilai 15 a yanzu. Ministan harkokin wajen Brazil Celso Amorim ya ce Japan ba ta goyi bayan sabon daftarin a hukumance ba. Kasashen dai na son a kara yawan membobin kwamitin sulhu daga 15 zuwa 25 sannan a kara yawan kujerun dindindin da wakilai 6.