1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gana tsakanin Chavez da Ahmedinijad a birnin Teheran

July 29, 2006
https://p.dw.com/p/Buoi

Shugabannin nan biyu da suka ki lamirin Amirka wato Hugo Chavez na Venezuela da Mahmud Ahmedi-Nijad na Iran sun gana yau asabar a birnin Teheran, inda suka karfafa aniyar ba juna hadin kai. Ziyarar yini biyu da Chevez ke kaiwa Iran ta zo ne a lokacin da gwamnati a Teheran ke shan sabon suka daga kasashen duniya game da shirin ta na nukiliya da kuma zargin ta da taimakawa mayakan kungiyar Hisbollah dake fafatawa da Isra´ila. A jiya dai kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu sun amince da wani daftarin kuduri wanda ya bawa Iran wa´adin zuwa ranar 31 ga wata agusta da ta dakatar da shirin ta na inganta sinadarin uranium ko kuma ta fuskanci barazanar kakkaba mata takunkuman tattalin arziki da na siyasa. Bayan tattaunawar da suka yi da shugaba Ahmedi-Nijad, Chavez ya ba da tabbacin cewa kasar sa zata ci-gaba da marawa Iran baya a kowane lokaci. A farkon wannan mako shugaba Chavez ya kulla yarjejeniyar sayen makamai daga Rasha, wanda hakan ya sha suka da kakkausar harshe daga Amirka.