1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gana tsakanin tawagar Afrika ta Kudu da bangarori masu gaba da juna a kasar Cote D´Ivoire

January 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9x

A birnin Abijdan na kasar Cote D´Ivoire an fara tantanawa tsakanin tawagar shugaban kasar Afrika ta Kudu Tabon Mbeki da bangarori daba daban masu gaba da juna, da tzumar samun mafita a rikicin da ke wakana a wannan kasa.

Tunni tawagar bisa jagoranci ministan tsaro na Afrika ta Kudu Mosioua Lekota, ta gana da shugaban kasa Lauran Bagbo, da kuma Praminsita Charles Konnan banny, saidai yan tawaye sun ki amincewa su amsa gayyata.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya, yan tawayen kasar Cote D´Ivoire, da a yanzu haka ke rike da arewancin kasar, sun zargi shugaba Tabon Mbeki, da nuna rashin adalci a cikin sulhun da ya ke.

A yayin da ya ke tantanawa, da manema labarai, shugaban tawagar Afrika ta kudu ,ya bayyana alamun amincewa da niyar da shugaba Lauran Bagbo ya dauka, na tazarce ga ,majalisar dokoki, sabanin matakin da komitin kasa da kasa, ya dauka na bukatar rushe wannan majalisa a karshen wa´adin ta.