1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gana tsakanin Thabo Mbeki da Angela Merkel a birnin Berlin

July 8, 2006
https://p.dw.com/p/BurC
Shugaban ATK Thabo Mbeki ya yi maraba da gudummawar da Jamus ke bayarwa a kasar JDK musamman ma wajen girke sojojin rundunar Bundeswehr. Bayan ganawar da yayi da SGJ Angela Merkel a birnin Berlin shugaba Mbeki ya ce duk wani ci-gaba da za´a samu a Kongo da kuma a Sudan yana da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar da kuma daidaituwar al´amuran siyasa a nahiyar Afirka baki daya. Wasu batutuwan da taron tsakanin shugabannin biyu ya tabo kuma sun hada da halin da ake ciki a Sudan da taron kolin kungiyar G-8 da zai gudana a karshen makon mai zuwa a birnin St. Petersburg na Rasha sai kuma batun shirin nukiliyar Iran da ake takaddama a kai. Merkel ta ce dukkan sassan zasu samu fa´ida idan Iran ta yarda da tayin taimako da KTT ta yi mata da nufin warware rikicin nukiliyar kasar.