1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawawwakin mutane 20 a wani babban rami a Lebanon

December 4, 2005
https://p.dw.com/p/BvIA

Hukumomi a kasar Lebanon sun fara bincike don shaida gawawwakin mutane 20 da mazauna wani kauye suka gano a cikin wani makeken kabari dake kusa da wata tsohuwar hedkwatar jami´an leken asirin Syria. Gawawwakin da aka gano a cikin wani rami dake a wani kwazazzabo sun kai akalla shekaru 12 a binne. Rahotannin sun ce daya daga cikin gawawwakin dai na sanye da unifom na sojin Lebanon. Kabarin na kusa ne da wani kurkuku, inda akan tsare firsinonin Lebanon kafin a kai su gidajen yarin Syria. Sojoji da jami´an leken asirin Syria dai sun kasance a cikin Lebanon tsawon shekaru da dama, gabanin wani bore da aka tayar a cikin watan afrilu wanda ya tilasta dakarun Syriar fice daga Lebanon.