1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cim ma daidaito kan cinikayyar duniya.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burz

5. An gaza cim ma daidaito kan cinikayyar duniya.

Manyan ƙasashe mafi arziki na duniya, sun gaza cim ma daidaito wajen amincewa da wani tsari, wanda zai bai wa ƙasashe masu tasowa damar cin moriyar cinikayyar ƙasa da ƙasa. A taron Ƙungiyar Ciniki ta Duniya da aka gudanar a birnin Geneva, an tashi ne dai ba tare da cim ma wata madafa ba a kan wannan batun. Wakilan ƙasashen da suka halarci taron, sun gaza yarjewa kan shawarar da aka gabatar, wadda ke bukatar ƙasashe mawadata su rage yawan tallafin da suke bai wa manomansu, sa’annan su ƙasashe masu tasowa kuma su buɗe kasuwanninsu ga kayayyakin da aka sarrafa daga ƙetare. Shugaban ƙungiyar Ciniki Ta Duniya Pascal Lamy, ya ce yanzu dai an shiga wani hali ne na taɓarɓarewar al’amura, amma duk da haka, ya yi imanin cewa, za a iya cim ma yarjejeniya a cikin ’yan makwanni masu zuwa, kafin lokaci ya ƙure.