1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza yin sulhu gabanin zabe a Burundi

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 19, 2015

Mahukuntan kasar Burundi sun tashi baram-baram a taron sulhu da ke zama shirin karshe na dakile yunkurin kawon karshen tankiyar siyasa da ta addabi kasar.

https://p.dw.com/p/1G1Gd
Al'ummar Burundi za su yi zaben shugaban kasa
Al'ummar Burundi za su yi zaben shugaban kasaHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Ngingo

Rikicin siyasa ya barke a Burundi ne sakamakon yunkurin yin tazarce da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ke yi. Tuni ma dai suka kawo tsaiko a tattaunawar a wannan Lahadi kwanaki biyu kacal gabanin zaben shugaban kasar mai cike da rudani.

Ministan harkokin cikin gida na Burundin Edouard Nduwimana ya ce sun bukaci kasar Yuganda da ke shiga tsakani da ta bayar da damar dakatar da tattaunawar, kana ya bayar da haske kan cewa akwai yiwuwar gwamnatin za ta fice daga tattaunawar baki daya. Dama dai 'yan adawar kasar ta Burundi sun sha alwashin kauracewa zaben shugaban kasar da za a yi a ranar Talata 21 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.

Wata majiya daga kungiyar kasashen yankin gabashin Afirka EAC da ta waklilta Uganda a matsayin bababar mai shiga tsakani a rikicin na Burundi, ta bayyana cewa ga dukkan alamu tattaunawar ta rushe baki daya kana ta yi gargadin cewa yanayin tsaro a Burundin ka iya dagulewa kowane lokaci daga yanzu.