1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An goyi bayan kamo wasu 'yan Sudan

June 12, 2010

Kwamitin Sulhun MƊD ya goyi bayan da a kame 'yan Sudan da ake zargi da aikata ta'asa a Darfur

https://p.dw.com/p/Np42
Sojojin sa kai a DarfurHoto: picture-alliance/ dpa

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa ta ce Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya na goyon bayan buƙatar kotun ta kamo wani gwamnan Sudan da wani madugun sojin sa kai da ake zargi da aikata ta'asa a lardin Darfur. Shugaban Kwamitin Sulhun a yanzu kuma jakadan ƙasar Mexiko a Majaliasar Ɗinkin Duniya Claude Heller ya ce ƙasashe 15 membobin Kwamitin sun amince cewa Sudan ta yi biyaya ga buƙatar kotun kana kuma ta miƙa mata gwamnan kudancin Kordofan Ahmed Haroun da shugaban sojojin sa kai na Janjaweed Ali Kushayb da ake zargi da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin Bil Adama.

Tun a shekarar 2007 Kotun ta ƙasa da ƙasa ta ba da takardar kame mutanen biyu saboda rawar da suka taka wajen aikata kisan ƙare dangi da tilastawa mutane tashi daga yankin na Darfur.

A nasa ɓangare shugaban masu shigar da ƙara na kotun Luis Moreno-Ocampo ya faɗawa Kwamtin Sulhu da ya tabbatar cewa MƊD da ta ba da fifiko wajen kame mutanen biyu a matsayin babban matakin samar da zaman lafiya a Darfur.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi