1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da zaɓen yan majalisa lami lahia a Burkina Faso

May 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuLt

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, a ƙasar Burkina Faso, ta ce, zaɓen yan majalisun dokoki da ya gudana jiya ga faɗin ƙasar baki ɗaya, an yi shi lami lahia.

A wajejn karhe 6 na yamma agogon GMT a ka rufe runfunan zaɓe kamar yadda a ka tsara tun farko.

Mataimakin shugaban hukumar zaɓe Adama Campaore, ya sanar manema labarai cewar, a nan take yanke, a ka fara ƙidayar ƙuri´u.

Shugaban tawagar yan sa ido na ƙungiyar taraya Afrika, ya bayyana gamsuwa a game da yadda zaben ya gudana salin alin.

Saidai Gerad Philipes ya ce yan samu yankura kura , wanda basu taka kara sun karya ba.

A na sa ran samun sakamakon ranar 12 ga watan da mu ke ciki.