1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da zaben sabon shugaban kasar Somalia---

Jamilu saniOctober 11, 2004

Masu lura da harkokin siyasar Somalia sun ce tilas ne sabon shugaba ya nemi hadin kan alumar Somalia baki daya----

https://p.dw.com/p/Bvfi
Hoto: dpa

Baban kalubalen dake gaban sabon shugaban kasar Somalia Abdullahi Yusuf a lokacin da ya zai koma gida daga kasar Kenya don kafa sabuwar gwamnatin da aka shafe tsawon shekaru 13 kamfin a kafa ta shine batun inganta tsaro a kasar ta Somalia.

Masana harkokin yau da kulum dake da masaniya a kann aiyukan kungiyoyin yan tawaye,da ake ganin su suka yawa a kasar Somalia,na hasahen cewar dukanin kungiyoyin yan tawaye da suka ga basu sami mukamin shugaban kasa ba a Somalia na iya kasara dukanin yunkurin da sabon shugaba Yusuf zai iya sanyawa a gaba na shimfida mulkinsa a birnin Mogadishu,birnin kuma da aka baiyana da cewar nada yawan kungiyoyin yan tawaye da yawan su ya kai 60,000.

Abu mai matukar wahala da ake ganin sabon shugaban kasar ta Somalia ya gada shine sake gina kasar da kuma dubum kudaden da gwamnati ke bukata da zata yi amfani da su wajen sake gina kasar ta Somalia da matsaloli na yaki ya dai daita.

Da yake jawabi kafin a zabi Yusuf a matsayin sabon shugaban kasar Somalia,wani mai sharhi kann alamuran yau da kulum na kasar Somalia mai suna Jabril Ibrahim Abdulle,ya baiyana cewar za’a fuskanci adawa mai tsananin gaske a sabuwar gwamnatin ta Somalia kuma abin tambaya shine ta yaya ne za’a dai daita tsakanin yan adawa da bangaren gwamnati a dangane da rabon madafun ikon wanan kasa.

Dukan sabon shugaban da yake son shimfida mulkinsa a Somalia tilas ne sai ya sami hadin kai daga kungiyoyin yan tawayen kasar,kafin a ce ya sami sukuni zuwa Somalia don kafa sabuwar gwamnati.

Yan majalisar dokokin Somalia sun gudanar da kada kuriun su wajen zabar sabon shugaban kasar Somalia a kann iyakar data raba kasar da birnin Nairobi,inda aka shafe tsawon shekaru biyu ana gudanar da taron tattaunawar sulhu da ake fatan zata kawo karshen rudanin siyasa da kasar Somalia ta shafe shekaru goma ana fama da su.

Shi kuwa Ken Menkhaus tsohowan mai baiwa majalisar dikin duniya shawara kann kasar Somalia wanda kuma a halin yanzu ke koyar da ilimin kimiyar siyasa a kwalejen Davidson ta arewacin Carolina,yace baban kalubalen dake gaban sabuwar gwamnatin Somalia shine tabatar da ganin ta dauki mataki na hade kawunan alumar kasar.

Kasar ta Somalia ta fada cikin rikici ne tun bayan da aka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Said Bare dan mulkin kama karya a shekara ta 1991.