1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gudanar da zaben shugaban kasa a Tunisia--

Jamilu SaniOctober 25, 2004

An baiyana Zine al-Abidine Ben Ali a matsayin mutumin da lashe zaben shugaban kasar Tunisia---

https://p.dw.com/p/BvfE
Hoto: dpa

A kasar Tunisia shugaban kasar mai ci a yanzu Zine al-Abidine Ben Ali da y shafi shekaru 17 yana rike da madafun ikon kasar,aka baiyana a matsayin mutumin da ya sami kashi 95 daga cikin dari na kuriun da alumar kasar ta Tunisiaa suka kada a zabukan shugaban kasa dana yan majalisun dokoki da aka gudanar a wanan kasa ta arewacin Africa duk kuwa da cewar yan adawa sun zargi cewar wanan zabe na ciki da magudi da aringizon kuriu.

Tsohon janar din sojin kasar ta Tunisia shine ya sake samun nasara hawaa kann karagar mulki na tsawon shekaaru biyar masu zuwa,bayan da ya sami gagarumar nasara a zabukan da aka gudanar na shugaban kasa dana yan majalisun dokoki a ranar lahadin data gabata,a yau litinin ne kuma maikatar cikin gidan kasar ta Tunisia ta bada sanarwar cewar Zine al-Abidine Ben Ali ya samu kashi 94.49 daga cikin dari na kuriun da aka kada lokacin zabe.

Sauran kuriun da aka kada lokacin zabe an raba su ne a tsakanin kanan jama’iyun yan adawa da suka hadar da yan takara irin su Mohammed Bouchiha,Mohammed Ali,Halouani,da kuma Mounir Beji.

Sauran yan jama’iyun adawa na kasar ta Tunisia sun baiyana takaicin su da sakamakon zaben dake nuna cewar Ben Ali ne ya lashe shi.Baban shugaban jama’iyar adawa na kasar ta Tunisia Nejib Chebbi da ya kauracewa zabe ya shaidawa kamfanin dilancin labaru na Reuters cewar,wanan sakamakon zabe da aka fitar bai dace da zaben irin na Democradiya ba illa dai tafiyar da tsarin mulki irin na malukiya na mutum daya tilo a wanan kasa ta arewacin Africa.

A lokacin da aka gudanar da manyan zabukan na shugaban kasa dana yan majalisun dokokin kasar ta Tunisia,ba’a baiwa kungiyar kare hakin bil adama ta kasar mai zaman kanta damar duba yadda aka gudanar da zabe ba,illa wasu jami’a kalilan na kungiyar kasahen larabawa da suka lura da yadda aka gudanar da zaben a wasu tashochin zaben kasar ta Tunisia.

Zaben da aka gudanar na jiya lahadi a kasar Tunisia,shine irinsa na na biyu da aka gudanar karkashin jama’iyu masu yawa,tun lokacin da kasar ta sami yancin kanta daga kasar Faransa a shekara ta 1956.

Ben Ali mai shekaru 68 da haihuwa ya kama ragamar mulkin kasar Tunisia ne a shekara ta 1987,bayan da aka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Habib Bourgiba da aka zarga da laifin rashin iya tafiyar da mulki.