1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gurfanar da sojin Britania saboda kin zuwa Iraki

Zainab A MohammadDecember 2, 2005
https://p.dw.com/p/Bu3j
sojojin ketare a Iraki
sojojin ketare a IrakiHoto: AP

Wani jamiin sojin Britania na fuskantar sharia a gaban kotun sojin kasar saboda kin amincewa da aiki a kasar Iraki.A jawaban kariya daya gabatar ,jamiin wanda ke zama kwararre ta fannin kula da lafiya yace,afakawa Iraki da yaki ,haramtaccen yunkuri ne.Idan har jamiin ya cimma nasara a dangane da shaidar da zai gabatara zaman shriaar da zaayi cikin wannan wata,to babu shakka zai iya haifar da illoli a manufofin siyasar kasar.

Flight Lieutenant Malcolm Kendall-Smith mai shekaru 37 da haihuwa,wanda ke aiki da sojin samana Britania yayi aikin rangadi sau biyu a kasar Iraki,kuma ya samu karramawa saboda irin rawa daya taka a ayyuka daya gudanar a kasar Afganistan a baya.

Amma bayan komowarsa daga rangadinsa na biyu a iraki,Kendall-Smith yayi nazari kan dalilan da suka haddasa aka afkawa Iraki da karfin soji,kuma ya gano cewa babisa kaida bane harin da aka kaimata,Kuma a shirya yake ya shiga gidan kurkuku a dangane da wadannan dalilai nasa.

Charles Heyman manazarci a sashin sadarwa na soji,dake kungiyar masu kare Flight Liutenant Smith.A nashi raayin Jamiin sojin yana da dalilai masu karfi

“A ganina yamna da batu,yana dalili domin Kofi Annan ya bayyana a MDD cewa afkawa iraki da akayi dayi da cigaban kasancewan sojoji a Kasar ,sun sabawa kaida,a dangane da kaidoji da akas gindaya a shariar Nuremberg a shekarata 1945”.

Kaidoji da aka gindaya alokacin shariar Nuremberg na daga cikin dokokin da kotun kasa da kasa dake sauraron manyan laifuffuka ke anfani dasu a yanzu haka.Kuma anyiwa dokokin gyaran fuska kamar hakan a kassshe 100 da suka hadar da Britania..Kuma dokar na bayanin cewa kirkiro hari na soji bawai laifi ne kadai babba ba,amma yana mai zama mafi girman laifi daya sabawa dokar kasa da kasa.Bayanan takardun da aka gano sun tabbatar dacewa,gwamnatocin dasuka jagoranci wannan yaki na Iraki,na sane cewa ya sabawa kaida.Misali,sakamakon taron daya gudana a Downing Street,watan fadar gwamnatin Britania a watan yulin shekara ta 2002.Shafi na farko na sakamakon taron yayi bayanin cewa,domin cimma wannan yunkuri na kaiwa iraki harin soji,dole a samu dalilai da zasu halalta hakan,kuma a halin yanzu babu wadannan dalilan.

Takardar dai tayi nuni dacewa ministocin Britania na sane cewa suna bada hadin kai domin kaiwa Iraki hari babu gaira babu dalili,kasar da bata zame barazana wa Amurka ko ita Britaniyan ba.

Chris Nineham daga wata kungiyar kare hakkin biladama mai zaman kanta,na ganin cewa Flight Liuetenant Kendall-Smith bazaiyi dogaro kadai kan wadannan shaida na kariya da Lauyansa zai gabatar ba.

Nieneham oton

“Ina ganin cewa nasarar da zai samu a wannan sharia,zai dogara ne da irin goyon baya dazai samu daga kowane mataki.Babu shakka,akwai masu goyon bayansa a soji,kuma yana da goyon bayan mafi yawan alummar Britania,domin akasarinsu na ganin cewa babu dalilan cigaba da kasancewar dakarun a Iraki,kamata yayi su komo gida,balle tura wasu sabbi.Idan ya samu wadannan goyon baya to yana tare da nasa”.

A hannu guda kuma Charles Heyman yayi imanin cewa ,idan akazo batun yakin iraki,akwai sabanin raayi da dama tsakanin sojojin.

Oton Heyman

“Har yanzu ban samu mutum guda a rundunar sojin Britania wanda yake ganin cewa harin Irakin ba kuskure bane,musamman tsakanin manyan jamiai”

A yanzu haka dai ana ganin cewa idan har Flight Lietenant Kendall ya cimma nasara a wannan shariar,to babu shakka sakamakonsa zaiyi wa wasu manya a gamnatin Britaniya Muni.

A ranar 5 ga watan Oktoba nedai aka fara gurfanar dashi gaban kotu,kuma anasaran cigaba da shariarsa acikin wannan wata da muke ciki.Kana masu lura da alamura dakaje suzo,babu shakka zasu cigaba da sanya idanu ayayin bayyanar Kendall-Smith a kotu.Idan kuma shaidunsa suka tabbata haiga bashi nasara,wannan shine zai fara kasancewa lokaci mawuyaci wa gwamnatocin Amurka da Britania akan Iraki.