1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gurfanar da wasu mutane uku a gaban kuliya a Biritaniya

August 30, 2006
https://p.dw.com/p/BulA

Har yanzu ana ci gaba da tsare da wasu mutane musulmai uku, da ke zargin nada hannu, a cikin shirin kai hari kann jiragen saman biritaniya da bai samu nasara ba.

An dai ci gaba da tsare mutanen uku ne bayan da aka kammala zaman farko na sauraren shari´ar su a wata kotu dake birnin London.

Ya zuwa yanzu dai a cewar yan sandan kasar mutane 15 ne aka tuhuma da hannu a cikin wannan hari da bai samu nasarar ba.

A kuma makon daya gabata, a cewar yan sandan, mutane takwas ne aka zarga da gudanar da munanan ayyuka, dake da nasaba da kokarin shiga da bama bamai da kuma tashin su a cikin jiragen saman na Biritaniya.

Daga dai cikin mutane 24 da aka cafke bisa zargin kai harin da bai samu nasarar ba, hudu daga cikin su an sake su ,biyar kuma har yanzu suna hannu.