1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka Falasdinawa 7 a wani hari da Isra´ila ta kai a Gaza

June 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buui
Falasdinawa 7 ciki har da kananan yara 3 da kuma mata aka kashe lokacin da wani jirgin ruwan yakin Isra´ila ya harba makamai masu linzami kan gabar tekun arewacin Zirin Gaza. Majiyoyin asibiti da wadanda suka shaida abin da ya faru sun rawaito cewa wadanda aka halaka sun je shakatawa ne a gabar tekun dake yankin Sudania lokacin da jirgin ruwan yakin Isra´ilan yayi musu lugudan wuta. Daga cikin wadanda suka rasun akwai wata mata da mijinta da kuma ´ya´yansu su 3. Wasu mutane 30 kuma sun jikata. A halin da ake ciki hafsan rundunar sojin Isra´ila ya ba da umarnin gudanar da bincike akan mutuwar Falasdinawan su 7. Wani kakakin rundunar sojin Isra´ila ya ce iya sanin su harin ba daga sojin sama ko na ruwa ya fito ba amma suna gudanar da bincike ko harin atileri ne. Kakakin ya ce ba su da tabbaci ko Isra´ila ce ta kai harin. A wani labarin kuma shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas yayi tir da wannan abu da ya kira kisan gillan da aka yiwa fararen hular Falasdinawa a Zirin na Gaza.