1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

201008 Bundeswehr Afghanistan

Küstner, Kai / New Delhi (NDR) October 21, 2008

Gwamnatin tarayyar Jamus ta yi tir da harin ƙunar baƙin wake da aka kai kan sojojinta a arewacin Afghanistan tana mai cewa aiki ne na matsorata.

https://p.dw.com/p/Fdvg
Ayarin motocin sojin Jamus a AfghanistanHoto: picture-alliance/ dpa

Ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier ya ce za a yi duk abin da ya wajaba don cafke waɗanda ke da hannu a wannan ta´asa.

A ´yan kwanaki ƙalilan da suka wuce majalisar dokokin Jamus ta ta ƙara wa´adin aikin sojojin ƙasar a Afghanistan sai ga shi a jiya Litinin an sake halaka sojojinta biyu da jiyawa ɗaya rauni a wani harin ƙunar baƙin wake da aka kan ayarin motocin sintirin rundunar Bundeswehr a lardin Kundus na arewacin Afghanistan. Wasu ƙananan yara biyar ´yan Afghanistan su ma sun rasa rayukansu sakamakon wannan harin wanda ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakin kaiwa.

Yayin da yake magana a birnin Berlin ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya bayyana harin da cewa aiki ne na matsorata marasa imani waɗanda ke goyawa Taliban baya.

Ya ce: "Aikinmu shi ne tabbatar da tsaro da gudanar da ayyukan ci-gaba da raya wannan yanki. Abin da muka sa gaba shi ne samun amincewar jama´a, kuma mun samu ci-gaba sosai a arewacin Afghanistan, to sai dai har yanzu ana cikin halin rashin sanin tabbas a yankin musamman dangane da irin waɗannan hare haren na ´yan ta´adda."

Ministan ya ƙara da cewa ya zama wajibi Jamus ta cika aikinta a Afghanistan domin idan ba a yaƙi ´yan ta´adda ba to za su yaɗu zuwa wasu yankunan.

A dai halin da ake ciki lardin Kundus na ƙara zama mai haɗari kamar yadda gwamnan lardin Injiniya Mohammed Omar ya nunar.

Ya ce: "A wannan yankin akwai ´yan Taliban da al-Qaida da yawa. Wannan yankin ya kasance wata cibiyar su a da. Taliban na tallafawa marasa aikin yi da kuɗi don su aiwatar da harin ƙunar baƙin wake."

An kai harin ne a wata unguwa dake kusa da garin Kundus inda a ƙarshen watan Agusta aka halaka wani sojin Jamus lokacin da motarsa ta hau kan wani bam. Duk da ƙaruwar hare hare kan dakarun Jamus a yankin ministan tsaro Franz Josef Jung ya yi watsi da kiraye kiraye da ake na janye sojojin Jamus daga wannan yanki. A gobe Laraba aka shirya yiwa sojojin jana´iza a Kundus.