1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka Yan fashi sama da dari bakwai a Najeriya

Ibrahim SaniNovember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CI6q

A tsawon watanni uku da su ka wuce, rundunar ´Yan sandan Najeriya ta halaka yan fashi da makami a ƙasar 785.Kakakin´Yan sanda na ƙasar Mr Haz Iwendi, ya ce al´amarin ya farune, a lokutan ayyukan jami´an tsaron ne, a gurare daban daban a ƙasar.A tsawon wannan lokaci a cewar Mr Iwendi, rundunar ta su ta kuma yi asarar Jami´ai a ƙalla 62. A yanzu haka a cewar kakakin akwai mutane dubu ɗaya da 561 da ake tsare dasu, bisa zargin ayyukan fashi da makami.Mr Iwendi ya ƙara da cewa, dazarar an kammala bincike a kan su, za a tusa keyarsu izuwa gaban ƙuliya. Rahotanni dai sun nunar da cewa rashin tsaro da ƙasar ke fama da shi nada nasaba ne da ayyukan yan fashi da makamin ne, a gurare daban daban a ƙasar.