1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hana 'yan kungiyar BBOG ganin Buhari

Ubale Musa/A'RaheemSeptember 6, 2016

A karon na biyu jami'an tsaro sun dakile yunkurin masu zanga-zangar fafufutukar ceto 'yan matan Chibok wato BBOG shiga fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

https://p.dw.com/p/1Jwfz
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in Chibok
Nigeria Demonstration Bring Back Our Girls in ChibokHoto: Reuters/A. Akinleye

A karon farko an kai ga gudanar da zanga-zangogi har guda biyu a tsakanin 'ya'yan kungiyar ceto 'yan mata 'yan makarantar na Chibok da kuma masu goyon bayan shugaban kasar da ranar yau 'yan sanda sun hana su karasawa. A gefe daya dai 'yan fafutukar ceto 'yan mata 'yan makaranta na Chibok da ke fadar gwamnatin kasar a karo na uku cikin tsawon makonni biyu ne yayin da a dayan bangaren kuma magoya baya na Buharin da a karon farko suka hallara a bakin fadar domin nuna goyon bayansu ga shugaban kasar da a cewarsu ke ta maza a cikin yakin yanzu suma ke yin zanga-zangar.

'yan fafutukar ceto 'yan matan Chibok
'yan fafutukar ceto 'yan matan ChibokHoto: Reuters

Sabon yanayin dai na nuna irin darewa gida biyun da ake fuskanta yanzu a bisa komai kama daga yakin cikin kasa na ta'addanci ya zuwa batu na tattali na arzikin Najeriyar. 'Yan fufutukar da suka tsallake shingen 'yan sanda har guda uku kafin da kyar da gumin goshi su kai ga isa fadar shugaban kasan Najeriyar Muhammadu Buhari dai sun ga ba zata. Kokarin barkewar rikici ko kuma demokaradiya ta fadar albarka ta baka dai, a nasu bangaren masu goya baya ga Buharin da suka zo da rigunan da ke dauke da goyon bayan nasu sannan kuma suna rera wakar goyon baya ga Buharin sun zargi masu fafutukar ceto 'yan matan da kokari na dauke hankali na gwamnatin daga nasarorin da ta samu a cikin yakin. Kara samun dama ko kuma alamu na gazawa dai, a wannan karon 'yan fafutukar sun yi nasarar lika hotuna na daukacin 'yan matan daya bayan daya a farfajiyar fadar da nufin aiken sakon cewar fa har yanzu 'yan matan suna dawa.

A hannun guda kuma bangaren jami'an tsaron da ke da alhakin ceto 'yan matan sun cafke sun kuma rike dan jaridar nan da suka bayyana cewa suna nemansa jim kadan da isarsa filin jsauka da tashin jiragen saman da ke Abuja. Ahmed Salkida dai na zaman mutum mafi kusa da yan kungiyar ta boko ta haramun da kuma akai amfani da shi wajen fitar da faifayen bidiyo har guda biyu na 'yan matan na Chibok. A yanzu dai, abun jira a gani na zaman tasiri na kama Salkidan a cikin nemo 'yan matan dama kila kare yakin da yai nasarar kare karfi na kungiyar amma kuma ya gaza kai wa ga fidda 'yan matan.

'yan fafutukar ceto 'yan matan Chibok
'yan fafutukar ceto 'yan matan ChibokHoto: Reuters