1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hau tebrin shawara tsakanin masu zanga-zanga da gwamnatin ƙasar France

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2v

Bayan gagaramar, zanga zangar da ta haɗa kimanin mutane million 3, jiya a ƙasar France, an koma yau tebrin shawara tsakanin haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadago, da na ɗallibai da kuma wakilan gwamnatin a hannu ɗaya.

Babban burin da wakilan ke bukatar cimma shine na samun mafita, a game da taƙƙadamar da ke wakana a France, a kan sabuwar dokar CPE,, wato Contrat Premiere Ambauche, dokan nan, ta ɗauka sabin ma´aikata, da ake ci gaba da kai ruwa rana kanta, a ƙasar.

Rikici a kan wannan doka, ya buɗa wani saban babe, a fagen siyasar Fance, wanda ke ƙara bayyana hamayya a fili, tsakanin Pramonista Dominique de Villepin, da ministan cikin gida, Nicolas Sarkozy, wanda a halin yanzu ,batun warware rikicin ya shiga hanun sa, a matsayin sa na shugaban jam´iyar UMP mai rinjaye, a majalisar dokoki.

Ƙungiyoyin ƙwadago da na yan makaranta sun yi tsaye, kan bakan su,na janye kwata- kwata wannan doka, a yayin da gwamati ,ya fi bukatar a yi mata kwaskwarima.

Jim kaɗan kamin fara tantanawar shugaban ƙasa Jaques Chirac, yayi kira ga kungiyoyin, da su bada haɗin kai, a kawo ƙarshen, wannan taƙƙadama, domin ba yan makaranta damar komawa bakin ajji, su shirye shiryen jarabawa, a yan kawanaki masu zuwa.