1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta fadin sakamakon zabe a Kongo

September 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bukb

Hukumar zabe ta kasar Kongo ta bayar da sanarwar jinkirta fadin sakamakon zaben yan majalisar dokoki, har zuwa ranar alhamis ta jibi idan Allah ya kaimu.

Sakamakon zaben da aka shirya fadi a farko farkon makon nan, an dage shine a cewar hukumar zaben bayan gano magudi da wasu jami´ai 10 suka yi, don bawa jam´iyyun adawa nasara.

Ya zuwa yanzu dai sakamakon bayan fage na nuni da cewa jam´iyyar hadin giwa da shugaba Joseph Kabila kewa jagoranci ce akan gaba da yawan kuri´un da aka kidaya.

Idan dai an iya tunawa, shugaba Joseph Kabila ne akan gaba a yawan kuri´u na zaben shugaban kasa, to amma ya gaza samun kuri´un da ake bukata domin lashe zaben.

Hakan yasa a watan gobe zasu sake karawa, a zagaye na biyu da mai rufa masa baya a yawan kuri´un , wato Jean Pierre Bemba.