1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jinkirta taron kafa gwamnatin hadin gwiwa a yankin Palasdiwa

Zainab A MohammadSeptember 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5F

An jinkirta tattaunawa tsakanin shugaba Mahmood Abbas da jammiyar mulki ta kungiyar Hamas ,adangane da nada gwamnatin hadin kann yankin palasdinawa.Taron da aka shirya gudanarwa a gobe talata ya samu jinkiri,inda wani babban jamiin fadar shugaban kasar Abu Rudneini,yace Mahmod Abbas bazaije zirin gaza kafin ranar laraba ba.Shirin kafa gwamnatin hadakan dai ya karaya,sakamakon kin laakari da Izraela da Hamas tayi,wanda kuma ke zama dalilin dayasa kasashen yammaci suka dakatar da tallafawa hukumar palasdinawan.Ayanzu haka dai kungiyar kasashen turai ta kaddamar da wani sabon shirin taimakawa wahalhalu na rayuwar alummar palasdinawan,inda take bada tallafin dala dubu 40 ta bankunan yankin.Kotun sojin iszaelan dai,ya zatar dacewa acigaba da tsare jamian gwamnatin Hamas guda 21 da aka cafke a wani rikicin daya barke tsakanin bangarorin biyu.