1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da bikin bude wassanin Francophonie a Jamhuriya Niger

December 7, 2005
https://p.dw.com/p/BvHW

A birnin Niamey na Jamhuriya Niger, yau ne a ka buda wassanin Francophonie.

A tsawon kwanaki 10 mahalarta wassanin, da su ka zo daga kasashen dunia, masu anfani da halshen Faransanci, za su takara ga wassanin motsa jiki daban daban, da kuma nuna al´adun su, na galgajiya.

Ministan wasani da al´adu na Faransa da ya wakilci shugaban Jacques Chirac ,ya ziyarci babbar assibiti birni Niamey, jim kadan kamin bikin bude wassanin.

Ya kuma bayyana wa shugaban kasar Niger Tanja Mamadu cewa, tawagar kasar Faransa, da ta kunshi mutane kimanin 200, ta yi tsumin kudade Euro dubu dari,domin taimakawa, a gina makaranta, da kuma sayen magani ga assibitocin Jamhuriya Niger.

A wani labarin kuma,jami´an tsaro,sun bayyana capke mutane 2,daga wanda su ka kashe wani dan yawan bude iddo, na kasar faransa a jihar Agadez, ranar 2 ga watan Desember.