1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da bincike game da kisan Benazir Bhutto

December 30, 2007
https://p.dw.com/p/Ci9Y

A ƙasar Pakistan an ƙaddamar da bincike na hadin gwiwa tsakanin jami’an ‘yan sanda da na tsaro da kuma fannin shari’a dangane da kisan shugabar adawa Benazir Bhutto.A dai ranar Alhamis aka kashe Benazir. Gidan TV na Pakistan ya fito da wani hoto dake nuna wani mutum na harbin bindiga mintuna kaɗan kafin tashin bam ɗin. Jamiyar Bhutto ta PPP tayi watsi da ikrarin da gwamnati tayi cewa ƙungiyar Alƙa’ida ce ta kashe Bhutto,tana mai baiyana cewa hukumomin suna ƙoƙari ne na kare rashin bada kariya ga Bhutto. A halin da ake ciki kuma ƙasar Jamus ta baiyana damuwarta game da ci gaban tashe tashen hankula a Pakistan tana mai gargaɗin cewa makamanta na nukiliya na iya faɗawa hannun masu tsatsauran ra’ayin islama.