1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da kwamitin bincike a Thailand

September 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuiZ

Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar Thailand, sun kaddamar da wani kwamiti na mutum tara , da zai duba zargin cin hanci da rashawa karkashin shugabancin Faraminista Thanksin Shinawatra.

A cewar kakakin sojin da suka yi juyin mulkin, Lt. Gen Palanggoon Klaharn, nan bada dadewa bane za´a fara rubuta sabon kundin tsarin mulki, da zai share fagen gudanar da zabe na gaba.

Bugu da kari kakakin sojojin ya nanata aniyar su ta tabbatar da doka da kuma oda a fadin kasar baki daya.

Haka kuma a cewar janar Palanggoon zargin da ake na sake gudanar da wani juyin mulkin, zuki ta mallau ce kawai, domin babu gaskiya a ciki.

Idan dai za´a iya tunawa an gudanar da juyin mulkin ne a lokacin faraministan kasar na halartar taron Mdd a birnin New york.