1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana fita dare a wasu biranen Faransa.

November 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvLt

A wata sabuwa kuma, mahukuntan wasu biranen Faransan sun dau matakan shawo kan tashe-tashen hankullan da ke barazanar yaduwa a duk fadin kasar, da kafa dokar hana fita dare ga duk matasa masu kasa da shekaru 16 da haihuwa. Dokar dai ta fara aiki ne a biranen Amien da ke arewaci da kuma Orléans da ke tsakiyar kasar. Tun jiya talata ne dai, gwamnatin Faransan ta kafa dokar ta baci na kwanaki 12, abin da ke bai wa kananan hukumomi damar kaddamad da dokar hana fita dare, da kuma bai wa jami’an tsaro damar tsare mutane ba tare da izinin kotu ba, da hana taron jama’a.

Rikicin Faransan dai ya barke ne bayan mutuwar wasu matasa, masu asali daga arewacin Afirka, a kwanaki 13 da suka wuce. Mafi yawan masu zanga-zangar, matasan musulmi ne, wadanda aka haife su a Faransan, suke kuma da fasfotunan kasar, amma wadanda ke ganin cewa sauran al’umman Faransan na nuna musu wariyar kabilanci da ta addini.