1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta baci a Carolina ta Arewa

Gazali Abdou TasawaSeptember 22, 2016

A Amirka Gwamnan jihar Carolina ta Arewa ya kafa dokar ta baci a duk fadin jihar a wani mataki na neman kwantar da tarzoma da ta barke biyo bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa wani mutun bakar fata

https://p.dw.com/p/1K6Nk
USA Polizei erschießt Afro-Amerikaner in North Carolina - Proteste
Hoto: Reuters/J. Miczek

Tarzoma ta barke ne biyo bayan kisan Keith Lamont Scott wani mutun bakar fata dan shekaru 43 da jami'an 'yan sanda suka bindige a ranar Talatar da ta gabata.

A saman shafinsa na Tweeter Gwamnan jihar ta Carolina ta Arewa Pat McCrory ya ce ya dauki mataki kafa dokar ta baci ne bayan da tarzomar ta kazanta a birnin Charlotte inda wani mutun ya ji munmunan rauni bayan da aka harbe shi da bindiga a lokacin zanga-zangar nuna adawa da kisan mutuman bakar fata.

Ana zargin jami'an 'yan sanda na birnin na Charlotte da bindige Keit Lamont Scott din bayan cewa ba shi dauke da makami. Sai dai jami'an 'yan sandar na masu da'awar cewa sun harbe shi ne bayan da ya ki ya saki wani makami da yake rike da shi lokacin da suka nemi kama shi.

Wannan lamari dai ya zo ne a daidai lokacin da a kasar ta Amirka ake zaman doya da man ja tsakanin ba bakaken fata da kuma jami'an 'yan sanda farar fata da ake zargi da aikata kisan ba gaira ba dalili kan bakaken fata a kasar.