1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta baci a Ethiopiya

October 9, 2016

Gwamnatin kasar Ethiopiya ta kafa dokar ta baci ta tsawon watannin shida a duk fadin kasar, biyo bayan tashin hankalin da aka yi a makon jiya.

https://p.dw.com/p/2R3bs
Firaministan Ethiopiya Hailemariam Desalegn
Firaministan Ethiopiya Hailemariam Desalegn Hoto: Getty Images/AFP/K. Desouki

An dai dau wannan doka ce bayan taron majalisar minitocin na jami'an gamnatin inda aka tafka muhawar mai surfi a game da asarar rayuka da kadarori da aka samu a sakamakon zanga-zangar da a ka yi. A ranar biyu ga watan Oktoba wani bikin al'adu na addini da aka yi a  garin Oromo da ke a yankin tsakiyya na kasar ya rikide ya koma zanga zangar kyamar gwamnatin wanda a ciki mutane 55 suka mutu.Sama da shekaru 25 ke nan da 'yan kabilar Oromo da Amhara na Ethiopiya wadanda sune ke da rinjaye a kasar ke jagorantar boran adawa da gwamnatin saboda abin da suka kira wariya da ake nuna musu.