1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta baci a Tchadi

November 13, 2006
https://p.dw.com/p/BucC

Gwamnatin chadi ta kafa dokar ta baci a babban birnin kasar ta Njamena da wasu garuruwa dake gabashin kasar.Wannan doka ya biyo bayan barkewan fadan kabilanci ne daya kashe daruruwan mutane a yan makonni da suka gabata.Gwamnatin kasar ta zargi zargi mayakan larabawan sudan da ruruta wsutan rikici tsakanin Lasrabawan tchadin,da takwarorinsu da ba yan kasa ba,ta hanyar hanyar kai somame garuruwan gabashin chadin,wanda ke kann iyaka da lardin Darfur din Sudan.Rahotannin kungiyyar gamayyar kasashen Afrika AU dai na nuni dacewa ,mutane 30 aka kashe kana wasu 40 sun jikkata ,alokacin kai wasu hare hare a kauyukan Darfur a karshen mako,harin da aka zargi mayakan larabawa na janjaweed dake marawa gwamnatin khartum baya,da aiwatarwa.