1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar tabaci a birnin Bagadaza

June 23, 2006
https://p.dw.com/p/Buss

A dangane da dauki ba dadi da ake ci-gaba da samu tsakanin sojojin sa kai daban daban da kuma jami´an tsaro, gwamnatin Iraqi ta kafa dokar ta baci tare da hana fita a babban birnin kasar. Hakan ya zo ne bayan wasu ´yan bindiga suka toshe hanya kana suka bude wuta akan ayarin motocin sintiri na sojin Amirka da na Iraqi a babban birnin. A kuma can garin Habhib dake arewa da birnin Bagadaza akalla mutane 12 sun rasu lokacin da wani bam da aka dana a gefen hanya ya fashe a wajen wani masallacin ´yan sunni. A garin na Habhib ne dai dakarun Amirka suka halaka shugaban al-Qaida a Iraqi Abu Musab Al-Zarqawi kimanin makonni biyu da suka wuce. A kuma can birnin Basra mutane sun rasa rayukansu a wani harin bam da aka kai da mota. A wani labarin kuma FM Iraqi Nuri al-Maliki ya saki karin firsinoni 500 daga gidan kurkukun Abu Ghraib. FM ya ce ya dauki wannan mataki wanda shi ne irinsa na 5 a wani yunkuri na yin sulhu da ´yan sunni.