1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar tabaci a yankunan dake fama da bala´in ambaliya a Filipins

December 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuZG
Shugabar Filipins Gloria Arroyo ta kafa wata doka da ta kira ta bala´i ya afkawa kasar bayan da ambaliyar ruwan nan da ruwan sama hade da iskar suka janyo ta halaka adruruwan mutane. A halin da ake ciki ana yi binne mutanen da bala´i ya shafa a kauyuka da dama na kasar. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an tabbatar da mutuwar mutum 400 yayin da wasu kimanin 400 kuma suka bata. Ana fargabar cewa yawan wadanda zasu mutum zai dara haka. Kusan mutane dubu 30 sun rasa gidajensu yayin da har yanzu a wasu wuraren ake fuskantar katsewar wutar lantarki da wayoyin tarho sannan kuma babu hanyoyin shiga cikin su saboda rushewar gadoji da lalacewar hanyoyin mota.