1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa sabuwar gwamnati a Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeDecember 29, 2005

A jiya ne sabon Prime Ministan Ivory Coast Charles Konan Banny,ya kafa sabuwar gwamnati,wadda ta hada da shugabannin adawa da kuma shugabannin tsoffin yan tawaye na kasar,inda yayi alkawarin samarda zaman lafiya da hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/Bu2t

Charles Konan Banny ya kuma yi alkawarin maiyarda kasar ta yammacin Afrika bisa turbar samarda zaman lafiya da hadin kai,bayan shekaru na yakin basasa,tare kuma da tabbatar da gudanar da zaben shugaban kasa cikin yanci da walwala a watan nuwamba na shekara mai zuwa.

Tun bore na watan satumban 2002,yan tawaye suke rike da arewaci da kuma wani bangare na yammacin kasar ta Ivory Coast,kuma tun daga wancan lokaci ne kasar mai kyakkyawar makomar tattalin arziki a yankin Afrika ta yamma ta rabe gida biyu.

Karkashin kudirin komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1633,sabon Firayim Ministan rikon kwaryan yana da cikakken iko akan dukkan harkokin tsaro,zabe da tattalin arziki,kuma yana da ikon saukad da duk wani minista da yaki bada hadin kansa.

An kuma dora masa nauyin kula da shirin kwance damara tare da tarwatsa kungiyoyin yan tawaye da kuma shirya zaben shugaban kasa,amma shi ba zai tsaya takara ba.

Sabuwar majalisar da ya kafa jiya laraba,tana da membobi 32,a maimakon 40 na tsohuwar gwamnatin da aka kafa a 2003 bayan yarjejeniyar Marcoussis da bata samu nasarar samarda zaman lafiya a kasar ba.

Yayinda jamiyar dake mulki ta (FPI) ta samu maaikatu 7,jamiyun adawa na RDR da PDIC kowannensu ya samu maaikatu 5,kujeru 6 kuma ga tsoffin yan tawayen kungiyar New Forces.

Shugabannin yan adawa dai sun baiyana farin cikinsu da sabuwar gwamnatin,suna masu fadin cewa,yadda aka tsara ta ba zaa samu wata matsala ba a halin yanzu.

Bayan kwanaki na tattunawa,an yanke shawarar cewa Konan Banny,tsohon gwamnan babbn bankin kasashen yammacin Afrika,shi zaa baiwa mukamin ministan kudi na kasar ta Ivory Coast,matsayin da ada Paul Bahoun Boubre na jamiyar FPI dake mulki yake rike da shi.

A yanzu haka Boubre an bashi matsayin ministan tsare tsare da harkokin ci gaba,yayinda sauran membobin jamiyarsa aka basu kujerun maaikatun kula da hakr maadinai,hadin kan kasa,ilmi,kula da dabbobi aiyukan gwamnati da kuma maaikatar kula da kare yaduwar cutar kanjamau.

Shi kuma guillaume Soro,shugaban kungiyar yan tawaye na New Forces an bashi mukamin ministan kula da sake gina kasa kuma shine yake a matsayi mafi girma na biyu na majlisar ministocin,an kuma baiwa jamiyarsa kujerun maaikatun sharia,ciniki yawon shakatawa da maaikatar kula da suka jikkata a lokacin yaki.

Kodayake matasa da suke goyon bayan shugaba Laurent Gabgbo abin bai musu dadi inda suka gudanar da zanga zanga na kin amincewa da nade naden da Banny yayi,suna kuma zarginsa da kwace muhimman maaikatu 2 daga hannun magoya bayan Gbagbo,ya kuma sanya manyan shugabannin kungiyoyin tawaye da suke rike da arewacin kasar.

Kafa sabuwar gwamnatin zata baiwa Gbagbo damar shirya zabe da kwance damarar kungiyoyin yan tawaye karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya data nada shi Firayin Minista a watan daya gabata,wadda kuma karkashinta ne aka baiwa Gabgbo damar ci gaba da shugabancin kasar bayan karewar waadin shugabancinsa na shekaru 5 a ranar 30 ga watan oktoba ya cika,har sai an gudanar da zabe a kasar mai arzikin Koko data rabe tsakanin yan tawaye da gwamnati.