1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a birnin Midyat na Turkiyya

Gazali Abdou TasawaJune 8, 2016

Mutane uku sun mutu a harin ta'addanci da aka kai a wannan Laraba da wata mota shake da ababe masu fashewa a ofishin 'yan sanda na birnin Midyat na kasar

https://p.dw.com/p/1J2ZR
Türkei Kilis Zerstörungen nach Raktenangriff
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A Turkiyya dan sanda daya da wasu fararan hula biyu sun halaka a yayin da wasu mutanen kimanin 30 suka ji rauni a cikin wani harin ta'addanci da aka kai a wannan Laraba da wata mota shake da ababe masu fashewa a ofishin 'yan sanda na birnin Midyat na kudu maso gabashin kasar.

Tuni dai firaministan kasar ta Turkiyya Binali Yildirim ya dora alhakin kai wannan hari ga 'yan tawayen Kurdawa na Kungiyar PKK. Tashar talabijin ta CNN, ta kasar ta Turkiyya ta ruwaito cewa motar mai shake da ababe masu fashewa ta yi yinkiurin keta shingen tsaro na kofar ofishin 'yan sandar birnin na Midyat ne, amma nan take 'yan sandar da ke gadi wurin suka buda wuta kan direban motar wanda shi kuma ya tayar da bam din da ke a jikinsa.