1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 52 dai suka jikkata sakamakon wani harin bom

Kamluddeen SaniAugust 11, 2015

Masu aiko da rahotannin sun ce a kasuwar Sabon Gari na tsakiyyar hada -hada na jama'a a lokacin da harin bam ɗin ya tashi, a inda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1GDf4
Nigeria Bombenexplosion in Dukku Bus Rang in Gombe
Hoto: picture-alliance/dpa

Harin bam ɗin ya tashi ne da misalin ƙarfe ɗaya da rabi a gogon Najeriya a wata kasuwa cikin garin Sabon Gari da ke jihar Borno.

Kawo yanzu kimanin mutane 52 suka jikkata yayin da 47 suka rigamu gidan gaskiya waɗanda tuni aka kwashe su daga kasuwar zuwa wani asibiti mafi kusa.

Wani mai suna Kidda wanda ya ganewa idanuwansa abin da ya faru ya bayyana cewar kasuwar na cike da mutane da ke yin hada-hada a ciki lokacin da bam ɗin ya tashi.

 Kimanin mutane sama da 600 suka hallaka sakamakon kai hare hare da 'yan Ƙungiyar Boko Haram suke kai wa tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗare gadon mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu na sheakara ta 2015.