1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin bam kan ayarin motocin sojin Denmark a Afghanistan

June 23, 2006
https://p.dw.com/p/Busr

Babban hafsan sojin Denmark a arewa maso gabashin Afghanistan, Jesper Helsoe ya tsallake rijiya da baya a wani harin bam da aka kai a gefen hanya. Bam din ya fashe ne a wani wuri mai nisan kilomita 20 daga Faizabad a lokacin da ayarin motocinsa ke kan hanyar zuwa wani wuri da aka aikin samar da ruwa ga mazauna wani kauye. Rundunar sojin Denmark ta ce ba wanda ya samu rauni a wannan hari to amma mota daya ta lalace. Denmark dai na da sojoji 41 a Afghanistan da ke taimakawa a wani aikin gina hanya karkashin jagorancin dakarun Jamus. A kuma kudancin Afghanistan rundunar sojin Amirka ta ce dakarun da sojojin Amirka ke wa jagoranci sun halaka mayakan Taliban 14 a samamen da suka kai a lardunan Uruzgan da Helmand.