1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai harin gurnati akan ayarin motocin FM Gedi a birnin Mogadishu

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvMH
Jami´an kasar Somalia sun ce mutane biyu sun rasu sannan 12 sun samu raunuka lokacin da wasu ´yan bindiga suka jefa gurnati da wata nakiyar karkashin kasa akan ayarin motocin FM Ali Mohammed Gedi. Da farko wadabda suka shaida abin da ya faru sun ce mutum 3 suka mutu a wannan hari, ko da yake FM ba ji ko kwarzane ba. To amma Mohammad Ali Amero babban jami´in gwamnati ya ce rahotannin da ya samu kawo yanzu na nuni da cewa masu tsaron lafiyar FM biyu ne suka rasu amma yawan wadanda suka rasu ka iya zarta haka. An kai hari ne jim kadan bayan da FM Gedi ya isa Mogadishu babban birnin Somalia don gudanar da wata ziyara. Birnin dai na matsayin wani sansanin madugan sojin sa kai wadanda aka ba su mukamin ministoci a cikin gwamnatin rikon kwarya da ba ta samun karbuwa a tsakankanin dukkan al´umar kasar ba. Duk da harin dai FM ya ci-gaba ganawa da wakilan majalisar dokoki da ba sa ga maciji da juna.