1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wasu jerin hare-hare a birnin Maiduguri

Salissou BoukariOctober 14, 2015

Wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai wasu jerin hare-hare guda uku a wata unguwar birnin Maiduguri, harin da ya hallaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/1GnYM
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Rahotanni da ke fitowa daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno na cewa wasu sabin harin Bama-Bamai da aka kai a daren jiya a wurare uku da ke unguwar Sajeri, sun hallaka mutane da dama tare da jikkata wasu. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan wadanda ake zaton ‘yan Kungiyar Boko haram ne sun tada bama-bamai da ke daure a jikin su a wasu wuraran da jama’a ke taruwa. Saidun sun tabbatar cewa, a wannan karon wasu maza ne suka kai wadan nan hare-hare na kunar bakin wake saidai babu wanda ya iya tantance daga inda suka fito.