1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kakkabe Mzoudi daga tuhumar ta'addanci

June 9, 2005

Babbar kotun tarayya ta Jamus ta ce babu wata takamaimiyar shaidar dake nuna cewar Abdelghani Mzoudi daga kasar Moroko dan ta'adda ne

https://p.dw.com/p/BvbP
Mzoudi da Sadiq
Mzoudi da SadiqHoto: AP

A lokacin da yake bayani alkalin alkalan kotun Talksdorf ya ce ko shakka babu mutane da dama zasu yi mamakin rashin samun Abdelghani Mzoudi da wani laifi, amma fa ba zata yiwu wata kasa dake biyayya ga doka da oda tayi fatali da shikashikan da ta dogara a kansu a fafutukar murkushe ta’addanci ba. Lauya mai daukaka kara da sunan gwamnati ya bayyana kaduwarsa lokacin da babbar kotun jihar Hamburg ta saki Mzoudi a cikin watan fabarairun bara, wanda ya ce babban kuskure ne kuma wajibi ne a sake gabatar da shari’ar bisa zarginsa da laifin taimakawa wajen kisan gilla akan mutane dubu uku da kuma ba da goyan baya ga wata kungiya ta ‚yan ta’adda. Amma babbar kotun tarayyar ta fito fili ta bayyana cewar a karar da aka daukaka gabanta, babu wani sabon batu ko wata sabuwar shaida da aka gabatar, illa kawai nuni da kurakuran da aka ce alkalai sun tafka a babbar kotun jihar Hamburg. A binciken da tayi kuwa ba ta gano wani kuskure daga alkalan ba. A maimakon haka ta lura ne da yadda alkalan suka bi diddigin dukkan shaidar da aka bayar a game da Mzoudi, tun daga lokacin dalibcinsa har ya zuwa ga zamansa a sansanin ba da horo na kungiyar al’ka’ida a kasar Afghanistan, suka kuma tantance dukkan bayanan da suka tara amma ba su ga laifinsa ba. Shi dai lauya mai daukaka kara da suna gwamnati har yau yana kan bakansa na cewar sakin Mzoudi babban kuskure ne da bai kamata a lamunce masa ba. Ya kuma ci gaba da bayani yana mai cewar:

Wannan hukunci da wuya a hakura da shi ta la’akari da mutane sama da dubu uku da aka yi musu kisa na ba gaira. Amma tilas ne mu amince da hukuncin sabota an yanke shi ne a wata kasa dake biyayya ga tsarin doka da oda. Saboda ba zata yiwu ba a hukunta mutum akan abin da bai aikata ba a kokarin neman wani da za a dora masa alhakin wata mummunar ta’asar da ta wanzu, ko ta halin kaka. Wannan ba alheri ba ne ga duk wata kasa mai biyayya ga tsarin doka da oda.

A yanzun dai an ba wa Abdelghani Mzoudi wa’adin wasu ‘yan kwanaki kadan masu zuwa domin ya tattara nasa ya nasa ya fice daga Jamus, in kuwa ba haka ba za a fatattake shi daga kasar da karfin hatsi. Bisa ta bakin lauyarsa dai Mzoudi na alla-alla ya koma gida Moroso, kuma dama dai jira yake ya ga karshen wannan shari’a. Kawo yanzun dai ba’a taba samun wani rahoton dake nuna cewar kasar Moroso ta danka wani dan kasar ga mahukunta na ketare ba, in ji lauyar tasa, a mayar da martani ga masu fargabar cewar idan ya koma gida kasar Amurka zata nema da a mika mata shi domin ta tasa keyarsa zuwa sansanin gwale-gwalenta na Gwantanamo, inda take cin karenta babu babbaka wajen azabtar da fursinoni da keta hakkin dan-Adam.