1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wadanda suka kai hari a Mali

January 27, 2017

Hukumomin tsaro a Mali sun ce sun kama mutane uku wadanda ake zargi da kai harin ta'addanci a Gao da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

https://p.dw.com/p/2WU9i
Mali Anschlag in Gao
Hoto: Getty Images/AFP

Sojojin Faransa wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali sun kama mutane uku dangane da harin kunar bakin wake a arewacin Malin wanda ya hallaka akalla mutane 77. Ministan tsaron kasar Salif Traore ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Kungiyar al Ka'ida a yankin Maghreb ta ce mayakanta biyar suka kai harin na ranar 18 ga watan janairu a kan wani sansanin soji a Gao da kuma yaa jikkata wasu mutanen fiye da dari daya.

Farmakin ya nuna irin kalubalen da gwamnatin da kuma dakarun kiyaye zaman lafiya suke fuskanta wajen shawo kan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi a yankin hamada na arewacin kasar.

Rundunar kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA na da sojoji dubu 13 daga kasashe 123 a kasar ta Mali.