1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama 'yan makaranta a Burundi

Antonio Cascais/Abdourahamane HassaneJune 9, 2016

A Burundi hukumomi na tsare da wasu 'yan makarantar sakandare saboda yin batanci ga Shugaban Pierre Nkurunziza kan hotunansa da ke kan littattafan 'yan makaranta.

https://p.dw.com/p/1J3dI
Burundi Polizeigewalt - Polizei schlägt Jungen
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

A kan kusan daukacin littattafan 'yan makaranta a Burundi an samansu a mana hotuna Shugaba Pierre Nkuriziza. Abin da wasu daga cikin 'yan makaranta na garin Muramvya inda lamarin ya faru wadanda ke da kimani shekaru 14 zuwa 18.

Suka bi hotunan shugaban kasar a kan littattafansu suka yi masu zane-zane na batanci, wani wuri an jirgice hanci ko karkata kai ko baki na Shugabab Nkurunziza. Kana wani wurin an ja dogon gemu tare da rubuta kalamar "Nkurumbi" wanda a harshen gargajiya na kasar na Kirundi ke nufin labarin maras dadi domin yi tozali ga sunan zuru'ar Nkuruziza da ake wa lakabi da sunan labari mai dadi.

Burundi Schulbuchkritzeleien
Hoto: DW

'Yan makarantar na ajin sakandare 11 aka kama to amma daga ciki kotu ta yi sakin talala ga yara shida, uku mata da uku maza wadanda shekarunsu ba su kai na yin kaso ba.

Yayin da sauran wadanda ke da shekaru 18 ake tsare da su a gidan kurku na garin Muramvya da ke da nisan kilomita 50 daga gabashin birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar. Wata matar 'yar shekaru 40 ya nuna takaicin yadda aka lalata rayuwar yaronta bisa abin da ta kira zalunci.

Kafin haka ya afku dama a cikin watan Mayu da ya gabata gwamnatin ta dakatar da 'yan makaranta kusan 334 na ajin sakandare da Koleji (college) saboda batanci ga shugabannin a garin Rubiza kusa da birnin Bujumbura babban birnin kasar amma daga bisani gwamnati ta soke hukuncin 'yan makaranta da yawa ba su koma ba domin jin tsoron daukar fansa.

Burundi Gewalt und Proteste
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Asusun kula yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana damuwa game da wannan lamari na tsare 'yan makaranta a gidan kaso sannan UNICEF ya ce akwai 'yan maranta biyu da suka raunana sakamakon harbi da bindiga na 'yan sanda lokacin da suka yi zanga-zanga

Wannan dai shi ne karo na farko da ake kama yara wadanda shekarun ba su kai yin kaso ba a kasar ta Burundi da ta samu kanta cikin wani yanayi na tashin hankali tun baya da Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi tazarce a karshen wa'adin mulkinsa a shekarar bara.