1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kamamla taron kasashen Afirka da na Turai a rabat

July 11, 2006
https://p.dw.com/p/Buqq

Kasashe 57 na Turai da Afirka sun amince da wani gagarumin shirin rage kwararar ´yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai. Shirin wanda aka amince da shi a gun babban taron da sassan biyu suka yi a birnin Rabat na kasar Marokko ya tanadi ba da karin taimakon raya kasa ga kasashen masu tasowa na Afirka tare da Skarfafa hadin kai a yaki ga kungiyoyi masu fataucin ´yan Adam. Hakazalika an amince da kara daukar tsararan matakan tsaron kan iyakoki. To sai dai shirin bai yi bayani game da kudin da za´a ware ga wannan aiki ba.