1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala babban taro na shugabaninnin Afrika

July 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuHC

An kammala babban taro na kwanaki uku na shugabanin kasashen Afrika a birnin Accra na kasar Ghana,inda aka tattauna batun hadewar nahiyar baki daya.

Shugabannin na Afrika sun sha alwashin gaggauta hadewar tattalin arzki da siyasar nahiyar domin tabbatar cimmma burin samarda taraiyar Afrika.

Sai dai kuma sun yanke shawarar daukar watanni shida domin duba batun hadewar nahiyar,batu da shugaban Libya Muammar Ghaddafi da takwaransa na Senegal Abdullahi Wade suke ganin wani koma baya ne ga ci gaban yankin.

Su dai shugabanin byiu sun bukaci a gaggauta samarda gwamnati na bai daya a yankin suna masu baiyana cewa akwai bukatar Afrika tayi magana da murya guda cikin irin halinda ake ciki yanzu a duniya.