1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron Annapolis

November 28, 2007
https://p.dw.com/p/CU1f

Bayan taron zaman lafiya na yankin Gabas ta Tsakiya a Amurka,shugabannin Israila da na Palasdinawa zasu ƙaddamar da shwarwari na samarda zaman lafiya a fadar white house yau laraba.Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta sanarda haka bayan taron wadda a cikinta suka amince da kafa yantacciyar ƙasar Palasdinu nan zuwa 2008.Rice ta nanata kalaman Bush tun farko a ranar talata inda ya ce zaa magance dukkan batutuwa.Bush yace ya sadaukar da kansa ga samarda kafuwar ƙasar Palasdinu a yankin kafin ya sauka daga mulki a watan Janairu na 2009.

A halin da a ke ciki kuma kasar Rasha ce zata karbi baƙuncin baban taron na gaba kann wanzar da zaman lafiyar yankin.Kodayake minsitan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya faɗawa kafofin yada labaru na cewa ba a kammala amincewa kan rana ko kuma tsara ajandar taron ba.