1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron kasashen Kungiyar EU da na Larabawa a birnin The Hague

Mohammad Nasiru AwalDecember 1, 2004

Mahalarta taron kasashen kungiyar EU da na Gabas Ta Tsakiya da na yankin Tekun Bahar Rum da ake kira taron Euromed, sun ce taron ya yi armashi.

https://p.dw.com/p/BveM
Tamabarin kasashen Euromed
Tamabarin kasashen Euromed

Ba safai ne ake annashuwa a taron kasashen yankin tekun Bahar Rum dake gudana tsakanin kasashen KTT da na yankin GTT da kuma na arewacin Afirka, kamar a wannan karo a birnin The Hague ba. Mahalarta taron sun bayyana cewar taron yayi armashi. Sauyin shugabanci da aka samu a cikin hukumar mulkin Falasdinu ya sa ana kara yin kyakkyawan fatan da ba´a yi tsammani ba gabanin rasuwar Mallam Yasser Arafat a ran 11 ga watan nuwamba. Ministan harkokin wajen Isra´ila Silvan Schalom da takwaransa na Falasdinawa Nabil Shaath sun yi ta doki na a gaggauta komawa kan teburin tattauna shirin wanzar da zaman lafiya da aka katse tun a cikin shekara ta 2000.

Ko da yake Shalom ya yi takatsatsan, amma da zai so a koma kan teburin yin sulhu nan-take, domin bisa ga alama, hakan zai kara masa farin jini a idanun ´yan Isra´ila. Su kuwa Falasdinawa ba zasu so su yi riga malam masallaci ba, wato zasu fi son a koma shawararin ne bayan an zabi Mahmud Abbas a matsayin shugaban hukumar mulkin cin gashin don ya jagoranci tawagar Falasdinawa a wannan tattaunawa.

Ita kuwa sabuwar kwamishinar dake kula da huldodin ketare na kungiyar EU, Benita Ferrero-Waldner a cikin doki ta kwatanta kyakkyawan yanayi da ya wanzu a gun taron da ci-gaban da aka samu a taron birnin Oslo. Shi kuwa a nasa bangaren ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi sara ne tare da duban bakin gatari, inda ya nunar da cewa komai na iya canzawa cikin gaggawa a yankin GTT, musamman da zarar an kai wani harin ta´addanci sai murna ta koma ciki.

A duk shekara kungiyar EU na kashe dubban miliyoyin Euro a kokarin da take yi na fadada angizonta a yankin GTT, musamman a tsakanin kasashen Larabawa da Falasdinawa, inda farin jininta ya karu a shekarun baya-bayan nan. Duk da kalamai na yabo da ministan harkokin wajenta yayi, Isra´ila ta na zargin Turawan da fifita Falasdinawa a kanta. Yayin da su kuma a nasu bangaren kasashen Larabawa ke saka ayar tambaya game da gaskiyar Amirka, musamman bayan mamaye kasar Iraqi da kuma abokantaka dake tsakanin GWB da Ariel Sharon. A cikin shekaru 4 da suka wuce, sha´awar yin sulhu a rikicin Isra´ila da Falasdinawa da gwamnatin Amirka karkashin shugaba Bush ba ta nuna kadan ce. Domin tun bayan darewarsa kan karagar mulki shugaba Bush bai himmatu wajen yin sulhu tsakanin Isra´ila da Falasdinawa kamar tsohon shugaba Bill Clinton ba.

Ba wani abin ku zo ku gani da masu yin sulhun yankin GTT bangarori hudu wato kungiyar EU, Amirka, MDD da kuma Rasha zasu iya yi. Amma idan sassan dake rikici da juna suka so, kungiyar EU da Amirka ka iya kafa wani kwamitin yin sulhu, musamman kasancewar ko-wane bangare yana da wanda ya amince da shi tsakanin Amirka da kungiyar EU. Idan Amirka da kungiyar EU suka hada karfi da karfe to za´a kai ga tudun dafawa bisa manufar wanzar da zaman lafiya a yankin GTT. Saboda haka yana da muhimmanci biranen Washington da Brussels su ba juna hadin kai fiye da a lokutan baya. Hakazalika bai kamata a sakarwa sabuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Condolezza Rice wuka da nama ba. Su kuma kasashen Turai su manta da rashin jituwar da aka samu dangane da yakin kasar Iraqi don a ci da yankin GTT gaba. Ta hake ne kawai za´a kai ga tudun dafawa a shirin wanzar da zaman lafiya da ake wa lakani da taswirar hanya.