1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron kolin MDD game da harkar sadarwa a birnin Geneva.

Mohammad Nasiru AwalDecember 12, 2003
https://p.dw.com/p/Bvn8

Ajandar taron kolin na birnin Geneva ta sanya dogon buri a gabanta, musamman don cimma manufar da MDD ta sa gaba game da yiwa sabuwar fasahar sadarwa da yada labaru kwaskwarima sannu a hankali. Tun gabanin bude wannan taro na birnin Geneva, wasu sun yi sukar cewa wasu kasashe na amfani da sabbin hanyoyin sadarwa musamman intanat wajen mayar da wasu kasashe masu karamin karfi saniyar ware. To sai dai wannan zargi bai da tushe, domin kasashe kamar China ba sa ba da cikkakken ´yanci yada labaru. Ko shakka babu sabuwar fasahar sadarwa ka iya ba da gagarumar gudumawa wajen warware matsalolin tattalin arziki da na zaman jama´a da ake fuskanta a kasashe masu tasowa, kamar yadda sakatare janar na MDD Kofi Annan yayi bayani a jawabin bude taro na Geneva. To sai dai hakan ba zai ka ga cike babban gibin da ake akwai tsakanin kasashe masu tasowa ba da masu arziki ba, dole sai an yawaitar harkar zuba jari. Don cimma wannan matsayi, yanzu kasashe matalauta da masu arziki sun kuduri aniyar inganta harkar sadarwa tsakaninsu. To sai dai kasashe masu arzikin masana´antu ne zasu fi cin gajiyar wannan harka. A halin da ake ciki kasashe masu tasowa har yanzu kokari suke su kai ga wani matsayi na na ci-gaban fasaha don samun wani kyakkyawan yanayin bunkasar tattalin arzikinsu. Duk wadannan dai na cikin manufofin da wannan taro ya sa ba. Kamar yadda MDD ke bukata, dole sabuwar fasahar sadarwa ta dijital ta kai ga kowa da kowa musamman a kasashe masu tasowa, ta yadda hakan zai ba da damar magance matsalolin talauci, yunwa da sai inganta harkar ba da ilimi. Ko da yake taron na birnin Geneva ya amince da wadannan manufofin, amma bai samar da wata matsaya daya game da ya adda za´a samar da kudin tafiyar da waddannan ayyuka ba. Alal misali tarayyar Jamus ta tura wani karamin sakatare ne na majalisar, wanda haka ke nunawa a fili cewa gwamnatin wannan kasa ba ta dauki batun na harkar sadarwa da muhimmanci ba. Su kuwa a nasu bangaren kasashen yankin Skandinavia sun dauki harkar ta sabuwar fasahar sadarwar da muhimmanci, inda a halin yanzu suke kan gaba yayin da Jamus ke matsayi na 18 Amirka kuma na matsayi na 11. Ko da yake taron na birnin Geneva bai cimma manufar da aka sa gaba ba, amma ya fara tattauna batun inganta harkar sadarwa tsakanin kasa da kasa. Kuma nan da shekaru 2 masu zuwa za´a gudanar da irin wannan taro a birnin Tunis na kasar Tunisia.