1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron kolin shugabanin kasashen yankin Gulf

December 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvFk

Shugabannin kasashen yankin Gulf sun daukaka kira na bukatar ganin babu wata kasa a yankin Gabas ta tsakiya dake mallakar makamai na nukiliya.

Shugabannin sun yi wannan kira ne a karshen taron kolin su na kwanaki biyu da suka gudanar a hadaddiyar daular Larabawa, tare da bukatar kasar Iran ta bawa Mdd goyon bayan daya dace don warware takaddamar makaman nukiliyar ta.

Duk da wannan kira da shugabannin suka yi, sun shaidar da cewa matukar nukiliyar ta Iran ta zaman lafiya ce to ba ruwan su da ita.

Bugu da kari, shugabannin kasashen na yankin Gulf sun bukaci kasar Israela data shiga cikin yarjejeniyar kasashe na hana sarrafa makamin na nukiliya, tare da barin sifetocin bincike gudanar da aikin su a cikin kasar.