1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron muradun ƙarni a New York

September 23, 2010

A ƙarshen taron muradun ƙarni a New York sakatare-janar na MƊD ya bayyana sikankancewar cewa za a cimma biyan buƙata kafin wa'adin shekara ta 2015

https://p.dw.com/p/PLA7
Sakatare-Janar na MƊD Ban Ki MoonHoto: AP

A cikin jawabin da yayi a ƙarshen taron, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya yayi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan inganta lafiyar mata da ƙananan yara inda ya ce kamata yayi gwamnatoci da ƙungiyoyin ba da gaji da masu hannu da shuni su zamo abin koyi a fannin ba da taimako.

An tsai da shawarar samar da sama da dala miliyan dubu 40 a baya ga alƙawuran da aka ɗauka, domin inganta rayuwar mata da ƙananan yara. Waɗannan alƙawura za su tabbatar da samun kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen kula da lafiyar marasa galihu.

An kuma jinjina wa ƙungiyoyi masu zaman kansu a matsayin waɗanda ke bin hanyoyi masu sauƙi wajen taimaka wa marasa galihu. Stefan German jami'in ƙungiyar World Vision ya ce kashi 40 daga cikin ɗari na ƙananan yara na mutuwa ne sakamakon ciwon huhu da gudawa. Ƙungiyar World Vision ta keɓe dala miliyan dubu da miliyan ɗari biyar domin yaƙi da wannan matsala. To sai dai a cewar German wannan kuɗi ba zai wadatar ba. Don haka an daidata kan samar da wasu kuɗaɗe ta wasu kafofi daban. Akan haka yake cewa:

"Wannan dai ba wani kudi ne da ya taka kara ya karya ba".

A baya ga haka akwai kudin da ake sa ran samu a yayin wani taron karo karo da zai gufana nan da makkoni biyu wanda babban sakataren majalisar dinkin duniya zai jagoranta.

Ga baki ɗaya an amince da ƙudurin da aka tsayar a ƙarshen taron da. Annika Söder wakiliyar shugabar sashin kula da muradun ƙarni na ƙungiyar abincin duniya FAO ta yi kira ga ƙasashe mawadata da su kawo nasu taimako da kuma ƙasashe matalauta da su hada ƙarfi da ƙarfe a wuri ɗaya domin inganta matsayin rayuwarsu.

Shugaban Amirka Barack Obama shi kuma a cikin jawabinsa kira yayi da a samar da yarjeniyoyin kasuwanci da baƙi ɗayan kasashe za su ci moriyarsu yayin tattatunawar da za a yi a birnin Doha. Sai da ma aka tafa masa a lokacin da ya yi kira ga ƙasashe masu ba da agaji da su cika alƙawuran da suka ɗauka. Ya ƙara da cewa Amirka na shirin yin gyara ga manufarta na raya ƙasashe domin ba da taimako ga ƙasashen dake taimaka wa kansu da kansu.

"Muna canja dabarunmu domin cimma manufofin taimakon raya ƙasashe. Ko da yake mun ba da taimako na wani lokaci har yanzu da sauran aiki wajen inganta rayuwar aluma. Za mu mai da hankali ga miliyoyin jama'a da suka shafe shekaru aro aro suna dogaro akan taimakon abinci. Saboda da cewa hakan bai nufin ci gaba."

Obama ya ƙara da cewa a maimakon tattalin talauci wajibi ne a ƙirƙirar da hanyoyin fid da jamma daga ƙangin talauci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal